A kwanakin nan, maganar wani babban Maulidi da ake cewa Shugaba Tinubu zai shirya a birnin Abuja ta mamaye kafafen sada zumunta. Duk da haka, babu wata sanarwa kai tsaye daga fadar shugaban kasa kan wannan Maulidi; mutane ne kawai ke yayata labarin a shafukan sada zumunta.
A cikin birnin Abuja, an samu jita-jita cewa Shugaba Tinubu zai shirya Maulidi na musamman. Labarin ya yadu ne ta kafafen sada zumunta, inda ake ta fadin cewa taron zai tara shugabanni, ‘yan siyasa, mawaka, da fitattun malamai daga sassa daban-daban na Najeriya.
Abin birgewa, ana cewa fuskoki masu ”capacity” daga gwamnati da al’umma zasu bayyana, wasu ma ba a saba ganin su a irin wannan waje ba.
Sai dai, har yanzu babu wani tabbaci daga fadar shugaban kasa; babu sanarwa ko sheda da aka fitar game da wannan Maulidi.
Labarin yana yawo ne tsakanin masu amfani da internet da masu son sanin sabbin abubuwa, amma har ya zuwa yanzu hukuma ba ta tabbatar ba.
Idan har aka shirya, Maulidi din zai zama dama ga jama’a su ga haduwar manyan fuska, su ji wa’azi, nishaɗi, da zumunci. Amma har yanzu ana jiran tabbaci daga fadar shugaban kasa ko masu shirya taron.
Muhawara:
Idan har Shugaba Tinubu zai shirya Maulidi a Abuja, shin kai dan Izala ne ko Darika, zaka halarta?
Idan baka da tabbaci, kana ganin ya dace a shirya irin wannan taro? Ka ajiye ra’ayinka a comment section, mu tattauna tare! ArewaJazeera Na Alfahari Daku!






