Sau da yawa ana jin wasu mata suna korafin cewa hailarsu tana rikicewa ko kuma sun yi shekaru a aure ba tare da samun ciki ba.
Ɗaya daga cikin manyan cututtukan da kan jawo wannan matsala ita ce PCOS (Polycystic Ovary Syndrome).
Menene PCOS?
PCOS wata cuta ce da ke shafar aikin ƙwayayen mahaifa (ovaries).
A yanayi na al’ada, ƙwai na mace yana sauƙowa duk wata domin yiwuwar samun ciki.
Amma a wajen mace mai PCOS, wannan tsarin kan rikice, ƙwai ya kasa sauƙowa yadda ya kamata.
Idan ƙwai bai sauƙo ba, samun ciki zai yi wuya.
Alamomin PCOS
Wasu daga cikin alamomin da za su iya nuna PCOS sun haɗa da:
Rikicewar al’ada: haila tana zuwa ba bisa ƙa’ida ba
Ƙarin kiba: ƙaruwa a nauyin jiki ba tare da wani bayani ba
Ƙuraje a fuska: musamman waɗanda suka wuce na al’ada
Fitowar gashi a fuska ko ƙirji
Jinkirin samun ciki bayan aure
Abin lura shi ne: ba lallai mace ta nuna duk waɗannan alamomi ba.
Wasu na iya samun kaɗan daga ciki, wasu kuma ba tare da alamomi masu yawa ba.
Shin PCOS na da Magani?
Abu mai ƙarfafa gwiwa shi ne, ana iya sarrafa PCOS tare da taimakon likita.
Mata da yawa masu PCOS suna samun ciki bayan bin magani da shawarwarin ƙwararru.
Me Ya Kamata a Yi Idan Ana Zargin PCOS?
Ziyartar asibiti domin gwajin hormones da cikakken bincike
Bin dukkan shawarar likita
Rage yawan kayan zaƙi da soft drinks
Yin motsa jiki akai-akai
Amfani da magungunan da aka tabbatar da ingancinsu
PCOS cuta ce da ke shafar mata da yawa, amma ba hukuncin rashin haihuwa ba ce.
Da wuri-wuri gano matsalar da bin shawarwarin likita na iya taimakawa mace ta samu lafiya da damar haihuwa.






