
Rayuwar ma’aurata na fama da kalubale da dama, musamman a zamanin da fasahar zamani ke kara sauki da wahala a lokaci guda.
Wani al’amari ne da ya girgiza kafafen sada zumunta, an samu wata mata da mijinta ya ka mata tana kallon bidiyon batsa da daddare a gidan aurensu. Da mijin ya gan ta, hankalinsa ya tashi, inda ya dauki matakin sakin ta ba tare da wata doguwar muhawara ba.
Wannan al’amari ya jawo cece-kuce tsakanin jama’a, wasu na ganin matakin mijin ya yi tsauri, wasu kuma na goyon bayan daukar matakin saboda tsare mutunci da kimar sa yasa yayi hakan.
Masu sharhi da malamai sun shawarci ma’aurata da su kasance masu gaskiya da son juna tsakani da Allah, su guji abubuwan da za su iya karya amana ko jawo sabani.
Darasi daga wannan labari shi ne, ya kamata ma’aurata su kula da yadda suke amfani da fasahar zamani da abubuwan da za su iya cutar da zamantakewar aurensu. Sirrin gida da mutunci dukiyoyi ne da ya kamata a kiyaye, domin gujewa irin wannan rarrabuwar kawuna.
Karanta irin wadannan labarai da darussa a shafinmu don karin fahimta da ilmantarwa.








