A shafukan TikTok, wata muhawara ta taso dangane da rayuwar “Super Uwar Lissafi”, wanda aka dade ana tatsuniya da tsokana a kan matsalolin da ya fuskanta. Duk da tsokanar da aka yi masa, social media ta zamanto hanya ta sauya rayuwarsa, har manyan mutane sun fara saninsa suna taimakonsa.
A baya, an sha jin kalmomi na ban mamaki a shafukan sada zumunta game da Super Uwar Lissafi, inda wasu ke cewa yana da matsalar kwakwalwa ne, ba ya shiga jama’a, ko yi wanka sau da yawa. Amma hakan ba cin mutunci ba ne, sai dai irin farin cikin da wasu ke nunawa ganin yanda rayuwarsa ta dan gyaru saboda tasirin TikTok da sauran kafafen sada zumunta.
Yanzu, manyan mutane sun fara ganinsa a matsayin mutum, suna yi masa kirari, har suna iya taimaka masa.
Super yana shiga tarurruka, yana samun kyakykyawan mu’amala yana sa manyan mutane dariya da nishadi duk da cewa har yanzu ba zai iya magana daidai na tsawon minti biyar ba.
Wannan ci gaban yana kara masa kwarin gwiwa, yana rage wasu daga matsalolin da ya dade yana fuskanta.
Irin wannan sauyi ya taba faruwa ga wasu shahararru irin su Ale Rufa’i Bilget da Umar Bush, inda social media ta taimaka musu cikin sauya rayuwa. Yanzu, Super Uwar Lissafi ya taka rawa, an dauki hotonshi a wajen dinner na auren da yaran Rarara, Super yayi wa rawa kwanan nan.
Hakika, wannan sauyi ba karamin farin ciki ba ne ga masoya da mabiyansa. Allah ya saka wa wadanda suka taimaka masa da alheri, shi kuma Allah ya kara masa lafiya da daukaka.






