An Bashi Kudi Don Sayen Gida, Amma Ya Zabi Kara Aure – Magidanci Dan Zaria Yayi Abun Mamaki!

A Sabon Garin, Zaria, wani magidanci mai mata biyu da yara takwas mazaunin gidan haya.

Rayuwa na tafiya da wahala, amma yana kokari wajen kula da iyalinsa.

Wani abokinsa ya tausaya masa, ya bashi kudi mai yawa da niyyar ya saya gida domin ya fita daga wahalar haya.

Amma abin mamaki, magidancin bai saya gidan ba. Sai ya yanke shawarar kara aure, ya dauki kudi ya kara aure mata ta uku itama a gidan haya, ya kara girman iyali.

Wannan lamari ya girgiza unguwa, ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin makwabta da abokai.

Wasu na ganin ya kamata ya fara magance matsalar gidansa kafin ya kara aure, wasu kuma na ganin kaddara ce da Allah ya rubuta.

Labari mai daukar hankali da ke nuna yadda wasu ke fifita bukatun zuciya fiye da na rayuwa, da yadda shawara da kudi ke canza rayuwa a cikin al’umma.

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *