Jarumin Kannywood, Aminu Sharif Ahlan, ya bayyana cewa kashi 90% na mata ba soyayya ba suke nema, illa namiji mai wahala kamar jaki wanda zai biya bukatunsu. Ya kara da shawarwarin cewa maza kada su zama “jakin” da matsaloli. Shin wannan fahimta gaskiya ce ko zance ne na ra’ayi?
A wata zantawa da aka yi da Aminu Sharif Ahlan, yace kashi 90 cikin 100 na mata ba soyayya suke nema ba.
Bisa ga fahimtarsa, yawanci mata sun fi son namiji mai juriya, karfin hali, da wanda zai iya rike su ta kowane fanni, fiye da soyayya ta zuciya kawai.
Wannan magana ta janyo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke goyon baya, wasu kuma na musanta ra’ayin.
Gaskiya, a rayuwa, akwai mata masu son jin dadi da kulawa, hakazalika wasu na son namiji mai iya daukar nauyi, wanda zai ba su kariya da abubuwan jin dadinsu.
Duk da haka, soyayya da fahimta suna da matukar muhimmanci a kowacce dangantaka, ba wai dogaro ga karfi ko wahala kadai ba.
Me kake tunani game da wannan ra’ayi? Mata sunfi bukatar soyayya ko namiji mai juriya ne suke nema?
Ku cigaba da ziyartar jaridar Arewa Jazeera don samun ingatattun labarai, rahotanni, wasanni, rahotanni da kuma fadakarwa.






