Aure na buƙatar kulawa da sabuntawa kamar yadda ake kula da duk wani abu mai muhimmanci a rayuwa.
Daya daga cikin abubuwan da kan taimaka wajen ci gaba da ɗorewar soyayya shi ne canza salon kwanciya yayin jima’i cikin yarda da fahimta.
Wannan canji na da tasiri mai yawa ga jin daɗi, lafiyar jiki da haɗin kai tsakanin ma’aurata.
GARGADI:Wannan rubutu na ilimantarwa ne ga ma’aurata halal kawai. An rubuta shi domin ƙarfafa fahimta, natsuwa da jin daɗi a aure cikin ladabi, ba domin batsa ko sabawa addini ba.
Ga wasu muhimman amfanin hakan.
1. Ƙara Nishaɗi Da Sabon Sha’awa
Yin abu iri ɗaya kullum kan janyo gundura a hankali.
Canza salo daga lokaci zuwa lokaci:
Yana kawar da monotonous
yana ƙara nishaɗi
yana sabunta sha’awa a aure
Aure yana buƙatar sabbin dabaru domin soyayya ta ci gaba da ƙarfi.
2. Ƙara Fahimtar Juna Sosai
Yin salo daban-daban cikin yarda:
yana taimaka wa ma’aurata su fahimci juna fiye da da
yana sa kowanne ya san abin da ɗayan ke jin daɗi a ciki
Wannan fahimta na ƙara kusanci da zurfin soyayya.
- Taimakawa Lafiyar Jiki
Wasu salon kwanciya na iya taimakawa wajen:
rage ciwon baya ko matsin ƙugu
inganta motsin jiki
haɓaka zagayawar jini da ƙara kuzari
Saboda haka, canjin salo ba jin daɗi kaɗai ba ne, har da amfani ga lafiyar jiki.
4. Rage Gajiya Da Rikicin Zuciya
Idan ma’aurata suna yin abu ɗaya ba tare da sauyi ba: Sha’awa kan ragu
zuciya kan gaji
Canza salo yana sa su ji kamar suna sake sabunta soyayyarsu, wanda hakan ke rage damuwa da rikici.
A Taƙaice
Canza salon kwanciya a aure:
ba laifi ba ne idan halal ne
yana buƙatar yarda da fahimta
dole ne a guji duk abin da zai cutar, ɓata kunya ko sabawa addini
Aure mai dorewa yana ginuwa ne a kan fahimta, kulawa da mutunta juna.






