Fitaccen gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na duniya, Cristiano Ronaldo, ya jawo hankalin duniya bayan bayyana irin ƙayatarwar da yake samu daga addinin Musulunci.
A yayin da yake murnar cin ƙwallo a baya-bayan nan, an ga Ronaldo yana sujjada, alamar girmamawa da sha’awa ga addinin.
Ya bayyana yadda yake nazartar addinin Musulunci, yana mai cewa yana da burin yin ziyara zuwa ɗakin ka’aba, amma har yanzu bai samu damar hakan ba saboda wasu dalilai.
Yace a halin yanzu yana jin kansa tamkar ɗan ƙasar Saudiyya ne saboda yadda ake nuna masa ƙauna da mutunci.
Munayi masa fatan alheri
Ku ci gaba da bin jaridar Arewa Jazeera don samun sahihan labarai masu ƙayatarwa da ilmantarwa.






