Wasu maza ba su iya gane cewa ko mace tana son su. Suna cikin rudani. Wannan labari zai nuna maka alamomin da mace ke nunawa idan tana sonka da gaske.
- Tana Neman Lokacinka*
Mace mai sonka za ta nemi ta yi magana da kai, ta gan ka, ta san labarin yau da kullum. Ba ta jiran ka kira, ita ma tana kira. Idan mace ba ta neman lokacinka, wataƙila ba ta damu ba.
2. Tana Tunawa Da Ƙananan Abubuwa
Ta tuna abincin da ka fi so, launin da ka fi so, abin da ka faɗa watanni da suka wuce. Mace mai soyayya tana kula da komai game da kai.
3. Tana Kishi
Idan ta ji kin wata mace, ta yi tambaya, ta nuna damuwa – wannan soyayya ce. Mace da ba ta damu ba, ba za ta yi kishi ba.
4. Tana Goyon Baya
A lokacin wahala, tana nan. Tana ƙarfafa ka, tana taimaka maka, tana addu’a dominka. Ba sai komai ya yi kyau ba kafin ta kasance tare da kai.
5. Tana Magana Akan Makomar Ku Tare
Tana cewa “idan mun yi aure,” “idan muna da yara,” “a nan gaba.” Idan mace tana shigar da kai a makomarta, tana sonka da gaske.
Idan ka ga waɗannan alamomi 5, to wannan mace tana sonka. Kar ka ɓata ta. Amma idan ba ka ganin koɗaya, wataƙila lokaci ya yi da za ka sake dubawa.






