Shin ko kun san cewa Adam A Zango ya samu shahara a Kannywood tun kafin Ali Nuhu kirkiro kamfanin FKD? Ga wasu abubuwa masu ban mamaki da baku sani ba game da tarihin fitattun jaruman nan guda biyu!
A tarihin fina-finan Hausa, Adam A Zango ya yi fice tun kafin Ali Nuhu ya kirkiro FKD Productions.
Adam ya taka muhimmiyar rawa a fitattun finafinai irinsu RAGA, HIYANA, da MAYA—duk tun lokacin da Ali Nuhu kansa ke mataki na karatu a hannun Darakta Tijjani Ibrahim.\]
Duk da cewa dukkansu sun yi aiki tare a karkashin kamfanin Sarauniya, amfani da kalmar “uban gida” da Adam A Zango ke yi wa Ali Nuhu, alama ce ta girmamawa da alakar aiki ba wai saboda ya fi shi kwarewa ko tsufa ba.
Wannan ya nuna cewa daraja da tsarin aiki a Kannywood na dogara ne da jarin kai da kuma irin rawar da mutum ke takawa tun farko, ba wai shekaru ko sananne da kake ba.






