Wasu mazajen suna son budurwa kawai, amma bazawara tana da abubuwan da budurwa ba ta da su. Wannan postzai buɗe maka idanu.
- Tana Da Gogewa*
Bazawara ta san yadda ake mu’amala da maza. Ta san abin da ke sa miji ya yi farin ciki, abin da ke ɓata masa rai. Ba za ka kashe lokaci kana koyar da ita ba.
2. Ta San Abinda Take So
Budurwa tana cikin gwaji, ba ta san abinda take so. Amma bazawara ta san abin da ke sa ta yi farin ciki. Wannan yana sa dangantaka ta fi sauƙi.
3. Ba Ta Da Yawan Tsammani
Budurwa tana tsammanin komai ya zama kamar fim. Bazawara ta san gaskiyar rayuwa. Ba za ta damu ka akan ƙananan abubuwa ba.
4. Tana Da Haƙuri
Bazawara ta san cewa babu cikakken mutum. Ta koyi haƙuri daga dangantakarta ta baya. Za ta yi maka haƙuri fiye da budurwa.
5. Ta Fi Sanin Saduwa
Bazawara ta san yadda ake more saduwa. Ta san jikinta, ta san abinda ke sa ta gamsu. Za ta koya maka, za ku more tare.
6. Tana Da Kwanciyar Hankali
Ba ta da yawan kishi marar dalili, ba ta da tsoro marar tushe. Ta fi kwanciyar hankali a dangantaka.
Hadisin Annabi ﷺ
Annabi ﷺ ya tambayi Jabir: “Budurwa ka aura ko bazawara?” Jabir ya ce bazawara. Annabi bai tsawata masa ba, sai ya ce: “Don me ba budurwa ba, ku yi wasa da juna?”
Wannan yana nuna duka biyun suna da daɗi – kowannensu da nasa.
Bazawara ba abin kunya ba ce. Tana da abubuwan da za su sa aurenta ya yi daɗi. Kada ka raina ta.






