Wasu abubuwa da muke yi lokacin saduwa suna kashe daɗin. Muna yi ba tare da sanin hakan ba. Wannan labari zai buɗe muku idanu.
GARGADI: Ga ma’aurata ne kawai (18+)
Abubuwan Da Ke Kashe Daɗin Saduwa
1. Tsallake Foreplay
Shiga saduwa kai tsaye ba tare da wasa ba. Wannan yana sa mace ta rasa daɗi, wani lokaci tana jin zafi.
2. Yin Gaggawa
Saduwa ba tsere ba ce. Gaggawa tana hana gamsuwa, musamman ga mace.
3. Shiru Tsit
Ba magana, ba kuka, ba motsi. Wannan yana sa saduwa ta zama kamar aiki, ba jin daɗi ba.
4. Tunani Akan Wani Abu
Tunanin aiki, kuɗi, ko matsala lokacin saduwa. Wannan yana raba hankali, yana kashe sha’awa.
5. Rashin Tsafta
Wari mara daɗi, rashin wanka. Wannan yana kashe sha’awar abokin zama.
6. Kallon Waya
Wasu har suna kallon waya tsakanin saduwa. Wannan rashin kunya ne, yana kashe daɗi.
7. Yin Saduwa Iri Ɗaya Koyaushe
Matsayi ɗaya, lokaci ɗaya, wuri ɗaya. Wannan yana sa saduwa ta zama gundura.
8. Yin Barci Nan Take Bayan Gamsuwa
Musamman maza. Bayan gamsuwa sai barci, ba runguma, ba magana. Mata ba sa son haka.
Ku guji waɗannan kuskure, saduwarku za ta inganta. Ku yi foreplay, ku ɗauki lokaci, ku yi magana, ku more juna.






