Wasu maza suna tsoron saduwa da matansu mai ciki. Amma saduwa tana da fa’idoji ga mace da jariri. Wannan labari zai bayyana.
GARGADI: Ga ma’aurata ne kawai (18+)
Fa’idoji Ga Mace
- Rage Damuwa – Saduwa tana sa jiki ya fitar da hormones masu sa annashuwa
- Inganta Barci – Mace mai ciki tana samun barci mai kyau bayan saduwa
- Rage Ciwan Jiki – Saduwa tana sassauta jiki, tana rage ciwon baya da ƙafa
- Ƙara Jinin Jiki – Saduwa tana sa jini ya zagaya sosai, yana amfanar mace da jariri
- Ƙarfafa Dangantaka – Tana sa miji da mata su kasance kusa da juna
Fa’idoji Ga Jariri
- Annashuwar Uwa – Idan uwa ta yi annashuwa, jariri ma yana ji
- Ingantaccen Jini – Jinin da ke zagaya yana kai abinci ga jariri sosai
- Shirya Haihuwa – Saduwa tana taimaka wa mahaifa shirya don haihuwa
Lokacin Da Baza A Yi Saduwa Ba
- Idan likita ya hana
- Idan akwai zubar jini
- Idan mace tana jin zafi
- Idan akwai matsalar mahaifa
Saduwa da mai ciki ba haramun ba ce, ba cutarwa ba ce. Tana da fa’ida ga mace, jariri, da dangantakar aure.






