Faso ko kaushi a kafa matsala ce da mutane da yawa ke fuskanta. Tana sa kunya da rashin jin daɗi. Wannan labari zai nuna maku dalilan da ke haddasa ta da kuma hanyoyin magance ta cikin sauƙi.
Faso ko kaushi a kafa yana faruwa saboda dalilai kamar haka:
- Fatar kafa ta bushe sosai
- Rashin shafa mai musamman mai ɗan ruwa
- Taka ƙasa babu takalmi
- Zafi ko sanyi mai tsanani
- Kumburin jiki ko kiba sosai
- Wasu cututtuka kamar ciwon sukari
Yadda Za A Magance Shi:
- Shafa mai a kullum – Coconut oil ko man kadanya (shea butter) suna taimakawa sosai
- Jiƙa kafafu a ruwan dumi – Na minti 15, sannan a goge a hankali da dutsen kafa
- Takalmi masu laushi – A yi amfani da takalmi masu laushi da ke rufe diddige
- Guji tafiya kafa tsirara – Wannan yana ƙara bushewa da fasawa
Ƙarin Shawarwari:
- Sha ruwa da yawa don fata ta samu danshi
- A shafa mai kafin kwanciya da dare sannan a sa safa
- Guji sabulu masu ƙarfi a kafa
Idan matsalar ta ci gaba, a tuntuɓi likita musamman idan akwai ciwon sukari.
Don ƙarin labarai, ku cigaba ziyarci Arewajazeera.com






