Rayuwar aure na bukatar sirri da natsuwa musamman idan akwai yara a gida.
Yana da muhimmanci ma’aurata su tabbatar ba su damun hankalin ‘ya’yansu ko basu bai wa yara damar ganin su ko jin sautin su a lokacin saduwa ba.
Ga wasu dabaru masu sauki da amfani da zaku bi don kare sirrinku da lafiyar zukatan yara.
Hanyoyi Da Za Kubi Don Kare Sirrinku Lokacin Saduwa:
- Zaɓi Lokacin Da Yara Suka Yi Bacci:
Fara saduwa lokacin da kuke tabbatar yara suna baccin dare ko da rana. - A Rufe Kofa Ko Samar Da Sauri:
Ku tabbatar an rufe kofa da kulle, ku kuma samu hanyar rage sautin magana ko motsi. - Amfani da Blanket Ko Kayan Shafa:
Blanket ko kayan shafa za su iya rage jin motsin gado ko sauti a karamin daki. - Ayi Saduwa a Wani Wuri Daban:
Idan akwai yara dakin ku, zaku iya zaɓar wani wuri da yara ba sa shiga – kamar bathroom ko wani daki na musamman. - Hana Sautin Karfi:
Yi kokarin rage sauti lokacin saduwa. Idan dole, ana iya kunna fan, radio, ko AC don karyar sautin. - A lura da Yanayin Yara:
Duba ko yara suna kusa da dakin ko suna iya tashi a lokacin, ku yi hankali kada ku tada hankalinsu.
Kammalawa:
Bayar da muhimmanci kan sirri da natsuwa ba zai hana jin daɗin aure ko shaƙuwa ba.
Hanyar da kuka bi don kare yara daga ganin ku ko jin ku zai ƙara mutunta junan ku, da gina lafiyar zukatan yara.






