Yawanci mutane sukan fi yin saduwa da dare, amma binciken kimiyya da na rayuwar ma’aurata ya nuna cewa saduwa da rana – a safiya ko da tsakar rana – na da fa’idodi masu yawa ga jiki, kwakwalwa, da soyayya
Amfanin Saduwa Da Rana:
- Ƙara Kuzari da Fara’a:
Saduwa da safe ko rana na sanya mutum jin kuzari da annashuwa a duk rana, yana taimakawa rage gajiya da kasala. - Inganta Lafiyar Zuciya:
Jima’i a rana na motsa zuciya da jini, wanda ke taimakawa rage haɗarin ciwon zuciya da hawan jini. - Rage Damuwa:
A lokacin saduwa, sinadaran hormone kamar dopamine da oxytocin na fitowa, suna taimakawa rage damuwa da ƙara jin daɗi a zuciya da kwakwalwa. - Karawa Zumunci da Soyayya:
Saduwa da rana na ƙara dankon zumunci tsakanin ma’aurata, yana faranta rai da ƙarfafa amana. - Yana Sa Bacci Mai Inganci Da Dare:
Da yamma, jiki zai fi natsuwa, hakan zai kai ga samun bacci mai kyau da dare. - Inganta Ci Gaba da Aikin Rana:
Daga safe idan aka fara da saduwa, sau da dama mai zai ji yafito aiki da kuzari da nutsuwa.
Kammalawa:
Saduwa a rana – musamman da safe ko tsakar rana – na da fa’ida ta fuskar lafiya, dankon zumunci da jin daɗin rayuwa. Abin da ya fi muhimmanci shi ne a kula da tsafta, yarda da fahimtar juna domin lafiya da farin ciki.






