Sau da yawa maza na fuskantar yanayin da mata ke ce musu “ba yanzu ba” ko “ina jin gajiya” idan an nemi saduwa.
Ga dalilan da ke haddasa haka da yadda Musulunci ke koya mana fahimta da hakuri.
Aure falala ne a Musulunci, kuma fahimtar juna da hakuri su ne ginshiƙin soyayya.
Idan mace ta ce ba yanzu ba, ba takaici ne ko rashin so ba, akwai manyan dalilai da za su iya haddasa hakan:
- Gajiya ko rashin kuzari: cikin aiki ko gajiya ta ɗauke mata sha’awa.
- Ba ta cikin yanayin sha’awa: Wata mace tana bukatar a fara da kulawa, maganganu masu daɗi da shakuwa kafin a nemi saduwa.
- Matsalolin lafiya: Wata lokacin mace na jin zafi ko rashin lafiya, hakan ke rage sha’awa.
- Matsalolin tunani ko damuwa: Idan tana cikin damuwa ko yanayin da ba daɗi, ba lallai ta samu natsuwar saduwa.
- Rashin tsafta ko kulawa: Tsafta da kwalliya na ƙara masa sha’awa. Idan ba a kula ba, mace na iya jin ba ta so.
- Lokaci bai dace ba: Mace na son a fahimci lokatan da ta fi jin daɗi, ba lallai a nemi saduwa a kowane lokaci.
Yadda Musulunci ke koyar da namiji:
Manzon Allah (SAW) ya koya mana mu kyautata wa matanmu, da fahimta da hakuri a duk yanayi.
A nemi fahimta, a ba mace lokaci, a kara tattaunawa da nishaɗi kafin a nemi saduwa.
Fahimtar dalilan da ke sa mace ta ce “ba yanzu ba” zai ƙara dankon soyayya da zaman lafiya a gida.
Aure na da buƙatar kyakkyawan adabi, kulawa da hakuri gwargwadon koyarwar Musulunci.
Ku ci gaba da bibiyar Arewa Jazeera don labarai, sirrin ma’aurata da ilmantarwa!






