Aure ibada ne, zaman lafiya da jin daɗi na ma’aurata na buƙatar fahimta da adab. Ga abubuwan da bai kamata mace ta yi wa mijinta ba lokacin saduwa ba, domin ƙara dankon soyayya da raha a gida.
Musulunci ya koyar da kyakkyawar mu’amala da fahimtar juna a aure.
Ga wasu abubuwa da bai kamata mace ta yi wa mijinta ba a lokacin kusanci:
- Kada ki nuna gajiya ko rashin sha’awa – Maza na son mace ta nuna jin daɗi, farin ciki da kuzari.
- Kada ki yi magana mara daɗi – Maganganu kamar “ka gama ne?” ko “ina gajiya” na rage masa kwarin gwiwa.
- Kada ki janye jikinki – Amshi da motsin jiki na ƙarfafa soyayya.
- Kada ki yi wasa da waya ko yanke hankali – Rashin kulawa a lokacin soyayya na iya jawo fahimta mara kyau.
- Kada ki zarge shi da tambayoyin da basu dace ba – Misali, “wanene ya koya maka haka?” yana iya rushe yanayi.
- Kada ki guji tsafta da ƙamshi – Tsaftataccen jiki da ƙamshi na ƙara masa sha’awa.
- Kada ki manta da motsin jiki da kallo – Kallo mai daɗi da murmushi na ƙarfafa soyayya.
- Kada ki barshi ke yin komai shi kaɗai – Nuna kulawa da shiga cikin yanayin tare da shi.
Kula da waɗannan abubuwa na inganta soyayya, fahimta da nutsuwa a rayuwar aure.






