Yawan sanya hannu a gabanta yayin jima’i ko aikata wasu abubuwa makamancin haka na iya jawowa mata da miji illolin lafiya. Hanya ce dake shigar da kwayoyin cuta kai tsaye cikin farji, hakan yana iya illata zama lafiya da jin dadi a jima’i. Ga bayanin illolin da wannan dabi’a ke haifarwa ga mace da namiji.
Sanya hannu ko wani abu a gabanta yayin jima’i na iya zama hanyar yaduwar kwayoyin cuta. Ga illolin da ke iya shafar mace:
Ga Mace:
- Shigar kwayoyin cuta (infection): Hannu ba ya da tsabta sosai, yana shigar da kwayoyin cuta kai tsaye cikin farji.
- Ciwon mara: Infection na iya kaiwa mahaifa, ya jawo ciwon mara ko PID.
- Rashin ni’ima: Zafi, kaikayi da bushewar farji saboda kumburi da kwayoyin cuta.
- Fitar wari da ɗigo mara kyau: Yawaitar bacteria kan addaba mace da wari mara kyau.
- Rashin haihuwa: Infection da ya kai tube na haihuwa na iya hana mace zubar da kwai yadda ya kamata.
Ga Namiji:
- Kamuwar infection/Sanyi (STI): Infection daga mace na iya shafar namiji, ya haifar da kaikayi, zafi ko ciwo.
- Rashin ƙarfi da gajiya: Infection na rage ƙarfin jima’i.
- Fitar ruwa mara kyau: Ingancin maniyyi na iya raguwa.
- Kuraje ko kumburin azzakari: Yaduwar bacteria zai iya haifar da kuraje.
- Rashin saurin tashi: Infection na iya hana azzakari tashin daidai.






