Kumfa-kumfa da ake gani yayin jima’i a gaban mace abu ne da ke yawan faruwa. Yana da dalilai daban-daban, galibi ba matsala bane, kuma na iya samuwa saboda tsarin jikin mace da yanayin saduwa. Ga cikakken bayanin dalilan da ke haddasa kumfa yayin saduwa.
1. Yawan ruwa daga farji:
Idan mace tana da sha’awa, farjinta na fitar da ruwa mai yawa domin sauƙaƙa saduwa. Wannan ruwa na iya haɗuwa da iska, ta haka aka sami kumfa.
2. Saduwa mai ƙarfi ko daɗewa:
Idan saduwa ta kasance da motsi mai ƙarfi ko ta daɗe, iska na iya shiga cikin farji, haduwa da ruwan mace tana samar da kumfa.
3. Ruwan namiji da mace sun hadu:
Haduwar maniyyi da ruwan mace, musamman idan sun fi yawa, zai iya zama kamar kumfa ko sabulu.
4. Cikakken tsafta:
Farji mai tsafta da laushi na sauƙaƙa fitowar ruwa, wanda kuma ke sauƙaƙa kumfa.
Yana da mahimmanci a sani:
Wannan al’ada ce ta jiki, ba matsala ba ce matuƙar babu wari, zafi, bushewa ko kaikayi. Idan an lura da wasu matsaloli na lafiya, a tuntubi likita!






