Jarumar Kannywood, Fatima Hussain wacce aka fi sani da Maryam Labarina, ta bayyana damuwarta tare da fashewa da kuka game da matsalar sace ‘ya’yan talakawa a Najeriya. Ta jawo hankalin shugabanni da al’umma kan muhimmancin tsaro da kariyar rayuwar yara.
Maryam Labarina ta fitar da zazzafan bayani kan matsalar sace ‘ya’yan talakawa a Najeriya biyo bayan sace yaran makaranta da akayia Kebbi.
Ta bayyana cewa shugabanni sun gaza kare rayuwar al’umma.
Ta ce, “Shugabannin mu sun gaza. Idan har ba za su iya samar da tsaro ba, da a rufe makarantu gaba ɗaya tunda yaran dalibai sun dade suna fuskantar barazanar sace-sace a Najeriya.
A wannan lokaci, ba farashin abinci ake damuwa da shi ba – kowa na kokarin kare kansa da iyalinsa ne.”
Bayani na Maryam Labarina ya kara jaddada yadda tsoron sace-sace ya zamanto ruwan dare musamman ga iyalan talakawa a Najeriya.






