Rayuwar aure na bukatar hakuri, ladabi, fahimta da ilimi. Ga shawarwari masu amfani da za su tallafa wa mace ta zama uwargida mai inganta soyayya da zaman lafiya a cikin gidanta.
Wadannan shawarwari za su taimaka wa mata wajen samun zaman lafiya, farin ciki da ingancin aure:
- Hakuri
- Ladabi da biyayya
- Tsafta
- Iya girki
- Iya kwalliya da ado
- Nuna kauna ga ‘yan uwan miji
- Iya kyakkyawan lafazi
- Kula da gida da abinda ke cikin gidan
- Yiwa juna uzuri da adalci
- Kyakkyawan fahimta a tsakanin juna
- Rikon amanar juna
- Kula da kishiya
- Kula da mijin
- Kula da yara
- Karfafa soyayya gare shi
- Ki so mahaifansa kamar naki
- Ki rike ‘ya’yan daba ke kika haifa ba kamar naki
- Biyayya ga dukkan abinda yayi umarni matukar bai sabawa shari’a ba
- Rakiya da masa addu’a idan zai fita
- Faranta masa rai idan yayi fushi
- Yin magana mai dadi, tausasawa, da murya mai laushi
- Hakuri da godiya akan kyauta ko abu da ya baki
- Yin shiru idan yana magana
- Kada ki tona sirrinsa
- Neman izini idan za ki fita ko yin azumi
- Sake fuska idan kuna tare
- Iya salon girki
- Gama abinci akan lokaci, tare da shi yayin ci
Rayuwar aure na bukatar jajircewa, hakuri, da fahimta daga uwargida.
Shawarwari masu amfani suna inganta soyayya, zaman lafiya, da girmama juna tsakanin ma’aurata. Idan mace ta rungumi waɗannan
shawarwari, za ta samu gida cike da kwanciyar hankali da farin ciki. Mutunta juna da kula da gida na daga cikin ginshiƙan zamantakewar aure mai dorewa.
Allah ya kawo dawwamammen farin ciki da rahama a gidanku!






