Yawan mata da ke damuwa bayan saduwa da mijinsu don samun ciki, amma sai su ga maniyyi yana zubowa waje. Wannan na haifar da fargaba: shin hakan yana rage damar samun ciki? Ga bayanin gaskiya da abubuwan da ya kamata ki sani.
Da dama daga cikin mata sukan shiga damuwa bayan saduwa, musamman idan burinsu shine daukan ciki. Wasu har su kan yi tunanin cewa maniyyi ya fita yana nufin ba zai yiwu mace ta dauki ciki ba. Amma kimiyya da gwaninta sun tabbatar cewa ba haka bane.
1. Farji Ba Akwati Ba Ne Da Zai Rike Maniyyi Gabadaya
Yayin saduwa, namiji na sakin ruwan maniyyi fiye da abinda jikin mace ke bukata. Kadan daga cikin maniyyi ne ke bukata ya shiga cikin mahaifa domin yin fertilize na kwai. Sauran maniyyin da ke dawowa waje ba matsala ba ne – hakan dabi’a ne ta santsi da halittar farji.
2. Hakan Ba Ya Hana Daukan Ciki
Kwayoyin sperm suna shiga bakin mahaifa ne a cikin mintuna kadan bayan inzali. Kafin mace ma ta tashi daga gado, yara daga kwayoyin sperm tuni sun riga sun shiga, sun fara hanyar su zuwa cikin mahaifa. Saboda haka, ba sai an dauki mataki na musamman ba.
3. Ba Lallai Ba Ne Ki Damu
Dawowar wani sashi na maniyyi waje baya nufin ba za a samu ciki ba. Cikin jikin mace akwai matakai da yawa da ke kare sperm da taimakawa wajen daukar ciki idan Allah ya so.
Kammalawa:
Ki kwantar da hankalinki – dawowar maniyyi waje bayan saduwa hanya ce ta dabi’a. Idan kina kokarin samun ciki, ki karfafa zuciyarki, ki bi shawarwarin likita, kuma kada ki damu da irin wannan lamari. Ilimi da fahimta sune mabuɗin kwanciyar hankali da samun lafiyayyen aure.






