Aure da daren farko sun shahara da al’adu da zato na ganin jini a saduwa ta farko, musamman ga budurwa. Amma meye gaskiya game da wannan? Ga bayanan ilimi da zasu kawar da rudani tare da ilimantar da duka matasa da maza.
A al’adar wasu yankuna, an yarda cewa wajibi ne bayan ango ya sadu da amaryar sa a daren farko sai ya ga jini a gado, alamar budurcinta. Wannan tunani ya jima yana jefa mata da dama cikin damuwa, wasu har ana zarginsu da rashin mutunci ko karya amana muddin ba a ga jinin ba.
Akan nuna farin kyalle a idon jama’a ana murna da hujjar cewa “an ga jini”.
Amma gaskiyar kimiyya ta bayyana cewa ba duk mace ce ke fitar da jini a daren farko ba, duk da cewa ba ta taba saduwa da namiji a rayuwarta ba.
Dalili kuwa shi ne, budurci ko tantanin budurci (hymen) yana da bambancin tsari daga mace zuwa mace.
Wani yana dauke da kauri kuma yana rufe gaban mace sosai, wasu kuma yana da siriri ko kuma ba ya wurin tun fil’azal.
Haka kuma, wasu abubuwa kamar motsa jiki, hawan keke, rawa, ko amfani da wasu kayan tsafta kan iya sa tantanin budurci ya bar wurin mace tun kafin aure ba tare da ta san ta rasa shi ba.
Ga wasu ma, fatar tana cikin hankali sosai ba a rasa zub da jini sai an yi saduwa mai karfi da rashin jinkiri, wanda hakan na iya kawo rauni fiye da kamata.
Bugu da ƙari, ba kyau maza su nuna zafin rai ko zargi ga amarya muddin ba a ga jini ba a daren farko.
Ya kamata a fahimci cewa wannan lamari na da alaka da ilimin halitta, ba da halayya ko tarbiyya ba.
Hakanan, fahimta, hakuri, da kula a tsakanin ma’aurata na taka muhimmiyar rawa a zamantakewar aure.
Kammalawa:
Daren farko lokacin koyi ne, cike da fahimta da tausayi, ba lokacin hukunci ko zargi ba. Saboda haka, duk wata al’ada ko tunani da ke ganin wajibi ne a ga jini, ya kamata a duba shi da idon bincike da ilimi, ba ido na zargi ko nuna wulakanci ga mace.






