Fita ta goma ta sabon shirin barkwanci “Zafin Nema” Season 3 ta kara jan hankali! Rabe da Ilu, abokan gidadanci masu burin arziki, sun faranta wa masu kallo.
A wannan shahararren shiri na barkwanci, Rabe da Ilu—abokai biyu da komai nasu daya, tunani daya, lissafi daya, har da burin yin arziki—sun shahara wajen neman hanya na yin kudi cikin dariya da dabaru.
A sahun wannan Episode 10, garin kokarin cimma burinsu na samun kudi, sai rigima da rashin jituwa suka shiga tsakanin Rabe da Ilu. Wannan rikicin ya bayyana zahirin yadda burin arziki zai iya jefa mutane cikin sabani, amma a karshe abota da barkwanci suka mamaye.
Shirin yana ƙayatar da masu kallo, yana nuna muhimmancin abota, jajircewa, da kuma nishadi duk da mawuyacin hali.
Kalli bidiyon “Zafin Nema” Season 3 Episode 10 anan!






