Saduwa da mai ciki wata muhimmiya ce da ke buƙatar kulawa, fahimta da neman ilimi. Akwai abubuwa da ya kamata ma’aurata su sani don ba wa mace mai ciki kariya da kwanciyar hankali, da kuma kare lafiyar jariri.
Lokacin da mace keda ciki, wasu canje-canje na jiki da kwakwalwa na faruwa da ke tasiri rayuwar zamantakewau. Saduwa da mai ciki ba laifi ba ne, muddin babu wani cikas daga lafiyar ta(Ma’ana lafiyarta kalau, ba abunda ke damunta), kuma yana da alfanu ga lafiyar mata da zamantakewar aure.
1. Shawarar Likita Tafarko
Yana da kyau samun shawarwarin likita kafin ayi saduwa da mace mai ciki, musamman idan ciki yana da wata matsala, ko likita ya ba da wata hani.
2. Kulawa Da Jin Dadi
Dole ne mijin ya fahimci cewa mace mai ciki na samun gajiya, canjin jin daɗi, ko sauyin sha’awa. A kula da hanyoyin da suka fi mata dacewa, kada a tilasta wani abu da ba ta so.
3. Zabe Matsayi Mai Sauƙi
Masana sun ce mafi yawancin mata masu lafiya za su iya saduwa cikin wannan lokaci, amma ana bukatar zabi salon da zai fi kawo sauki da kwanciyar hankali – na jin jiki, ba nauyi a ciki, kuma ba zafi.
4. Karfafa Zumunci da Soyayya
Lokacin ciki yana da matukar muhimmanci ga dangantakar ma’aurata. Saduwa kan kara dankon soyayya, rage gajiya da damuwa, da karfafa zumunta a tsakanin miji da mata.
5. Girmama Bukatun Juna
Akwai bukatar mijin ya girmama damuwar matarsa, da jin tausayinta, har da taimakonta wajen dawowa hayyacinta da samun kwanciyar rai.






