Kwararriyar likita Maimuna Kadiri ta bayyana muhimmancin yawan saduwa tsakanin mata da mazajen su don samun lafiya, farinciki, da dankon soyayya. Ga dalilai 10 da ta lissafa!
Shugabar Pinnacle Medical Services, Dr Maimuna Kadiri, ta jaddada muhimmancin saduwa akai-akai tsakanin ma’aurata.
A cewarta, yawan saduwa na taimakawa lafiyar jiki da kwakwalwa, kuma yana inganta zamantakewar masoya.
Ta bayyana cewa mace kan fada cikin damuwa da rashin kwanciyar hankali idan ta gaza samun hakkinta na saduwa, yayin da matan da ke kusanci da mazajensu akai-akai ke jin sauki, farin ciki, da lafiyar zuciya.
Ga dalilai 10 da Likita Maimuna ta lissafa masu ƙarfafa saduwa tsakanin ma’aurata:
- Yana rage ciwon kai
- Yana kaifafa kwakwalwar mace
- Yana ƙara dankon soyayya
- Yana yaye damuwa
- Yana kwantar da yawan tunane-tunane
- Yana gyara lafiyar jiki
- Ana samun barci mai kyau
- Ana zama cikin farinciki a kullum
- Fatar mace na ƙara sheki da kyau
- Yana jan hankalin miji, samar da zaman lafiya da so tsakanin ma’aurata
Likita Maimuna ta ce matan aure su dage wajen kusantar mazajen su don amfanin lafiyarsu da ingancin rayuwar auren su.






