Sheikh Professor Isa Ali Pantami, Majidadin Daular Usmaniyya, ya kafa tarihi a jihar Gombe ta hanyar aiwatar da sama da ayyuka 170, ciki har da kafa cibiyoyin kimiyya, koyarwa, da fasaha tare da samar da guraben aiki ga matasa fiye da 600 a Najeriya.
A tsawon lokacin da Sheikh Professor Isa Ali Pantami ya jagoranci NITDA da kuma Ministan Sadarwa, ya gudanar da jerin ayyuka masu yawa a jihar Gombe—wani abu da ke da matukar tasiri ga al’umma da matasa
.
Babu wanda ya taba rike mukami a tarihin jihar Gombe yayiwa jihar ayyukan da suka kai kwatankwacin abin da Sheikh Pantami ya samu. Idan akwai, kawo misali a bayyane!
Wasu daga cikin jerin aikinsa sun hada da kafa ofisoshin cibiyoyin sadarwa, cibiyoyin koyar da fasahar zamani, daukar matasa aiki a wurare daban-daban, samar da tallafi da horo ga manoma, da inganta cibiyoyin koyon aiki da ilimi har makarantu masu tasiri.
Misalai daga cikin ayyukan:
- Kafa NCC, NITDA, Galaxy Backbone, da Nigerian Communications Satellite Limited Zonal Offices a Gombe.
- Create Digital Economy Centres & E-Learning a makarantun gwamnati da masu zabi daban-daban a Gombe.
- Samar da Base Transceiver Stations (BTS), cibiyoyin sadarwa da bunkasa Internet wireless a jami’o’i da polytechnics.
- Horas da manoma 565 a fannin Smart Agriculture tare da tallafi na N100,000 da na’urorin zamani.
- Samar da guraben aiki sama da 600 ga matasa ’yan asalin jihar.
- Gyara da inganta cibiyoyin sadarwa na NIPOST da NIMC a fadin jihar.
- Samar da School Knowledge Centres, da horar da matasa a VSAT da digital skill.
Sheikh Pantami ya kasance ginshikin bunkasar ilimi, fasaha, da ci gaban jihar Gombe.






