Kwadayin nishadi da fadakarwa ne ya ke koyar da fina-finan Hausa a baya, amma a yanzu masu kallo suna bayyana damuwa kan sabon salon da aka fara amfani da shi — wato shafa wa musulmi kashin ta’addanci a shirye-shiryen Hausa.
Masu kallo, musamman matasa, sun fara sukar wannan abu, suna cewa abu ne mai tada hankali domin yana iya bai wa wasu ra’ayi mara kyau game da musulmi, musamman ga masu bukatar shiga muusulunci.
Wasu na ganin cewa hakan guba ce ta shigo daga kasashen waje – inda ake alaƙanta ta’addanci da musulunci a fina-finan India da Pakistan, yanzu haka kuma sai ga shi an fara shigo da wannan akida a cikin fina-finan Hausa na gida.
Wani bangare na masu sharhi na tambaya: “Shin mene ne sakon da masu shirya shirin ke kokarin isarwa? Kina kokarin jawo kiyayya ce ko kuwa kawai kuskure ne da rashin tunani mai zurfi?”
Sauran na ganin wannan yana kara kaskantar da martabar musulmi a idanun duniya da mafaikun al’umma, musamman matasa.
Masu lura da cigaban masana’antar fina-finan Hausa na kira ga masu bada umarni da rubuta labarai da su rungumi gaskiya, su daina amfani da siffofi masu tsarki wajen nusar da mugaye ko barna a cikin shirye-shirye, musamman a irin wannan lokaci da ake da kalubale na rashin fahimta tsakanin al’ummomi.
Me Za Ku Iya Cewa?






