Jim kadan bayan da aka taba samun kuskuren kai hari a lokacin Maulidi a Tudun Biri, Kaduna, sojojin Najeriya sun dawo da kyautatawa, sun gina sabuwar makarantar firamare domin inganta ilimi a yankin.
A shekarun baya, rundunar sojojin Najeriya sun yi kuskuren kai hari kauyen Tudun Biri dake cikin Gundumar Rigasa, Kaduna, dai-dai lokacin da ake gudanar da Maulidi—inda harin ya fada ga masu shagulgula cikin bukin.
Bayan wannan mummunan lamari, al’ummar yankin sun samu tallafi da taimako daga manyan ’yan siyasa da attajiran Najeriya.
A yan kwanakin nan, sojoji sun dauki mataki na gyara dangantaka da al’ummar kauyen, inda suka gina sabuwar makarantar firamare a Tudun Biri.
Wannan makarantan ta zama wata alama ta komawa da tallafi, ci gaba, da inganta ilimi, tare da cike gibin da rikicin baya ya haifar.
Al’umma sun nuna godiya da karamci bisa wannan aiki na sojoji, tare da fatan hakan zai kara zumunci da zaman lafiya.






