Sabon rikici ya kunno kai a jam’iyyar PDP bayan tsagin Wike ya sanar da korar gwamnonin Bauchi (Bala Muhammad), Zamfara (Dauda Lawal), da Oyo (Seyi Makinde) tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar ciki har da sabon shugaban PDP, Tanimu Turaki, da Bode George.
A wata sabuwa da ta tsunduma jam’iyyar PDP cikin rikicin bangaranci, tsagin da ke goyon bayan ministan Abuja, Nyesom Wike, ya sanar da korar wasu fitattun jiga-jigan jam’iyyar.
Cikinsu har da gwamnan Bauchi, Bala Muhammad; na Zamfara, Dauda Lawal;
da na Oyo, Seyi Makinde. Hakazalika, an sallami sabon shugaban PDP da aka zaba, Tanimu Turaki, SAN, da tsohon mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar, Bode George.






