
Mata da dama ba su da tabbas musamman idan mijin ya dade bai dawo ba bayan yin aure. Wannan labari ya samo asali ne daga wata amarya da ta auri angonta, amma bayan watanni uku da aure, ango ya tafi kasar Libya, bai dawo ba har sai bayan shekara uku.
Da angon ya dawo, suka ci gaba da zamantakewar aure kamar yadda suka saba. Bayan watanni biyar, amarya ta fara fuskantar matsalar rariyar gidan—ruwa ba ya fita sosai. Tace wa angonta ya duba rariyar.
A karshe, angon yaje wajen abokinsa mai yin gini ya aro kayan aiki don gyara. Bayan ya bude rariyar gida sai ya ga condom ne ya toshe rariyar. Wannan lamari ya jawo tambaya: Shin ya dace angon ya fada wa amarya abin da ya gani, ko ya yi shuru su ci gaba da rayuwa kamar yadda suka saba?
Leave a Reply