Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika Mataimakinsa, Kashim Shettima, zuwa Jihar Kebbi domin jajantawa al’ummar jihar da iyayen ’yan matan da aka sace a Maga. Shugaban ya tabbatar da tsauraran matakai don dawo da tsaro da kwato yaran cikin gaggawa.
Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya sha alwashin cewa gwamnatin sa na kan kokari don kubutar da ’yan matan da aka sace daga makarantar sakandaren Maga a Jihar Kebbi.
Tinubu ya tura Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, domin jajantawa iyayen ’yan matan da kuma al’ummar Jihar Kebbi, tare da tabbatar da cewa gwamnati na aiki tukuru don dawo da tsaro a jihar da ƙasa baki ɗaya.
A cikin sanarwar mai ba shugaban ƙasa shawara kan labarai, Bayo Onanuga, an ce shugaba Tinubu ya jajanta wa rundunar sojin Najeriya bisa rasuwar sojoji da Birgediya Janar Musa Uba a Jihar Borno.
Shugaban ya nuna matukar damuwa da faruwar lamarin, tare da yin Allah-wadai da harin ta’addanci.
Ya bukaci al’umma, musamman a yankunan da ke fama da matsalolin tsaro, da su rika ba hukumomin tsaro bayanan sirri don taimaka musu wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Tinubu ya jaddada cewa hukumomin tsaro ba za su iya yin aiki yadda ya kamata ba tare da goyon baya da bayanai daga al’ummar yankuna ba.






