Hon. Nuhu Abdullahi ya bayyana a shirin Dokin Karfe TV cewa ba a taɓa samun shugaban ƙasa mai ƙauna da goyon bayan ‘yan Najeriya kamar Bola Ahmed Tinubu, musamman daga yankin Arewa. Shin kun yarda da wannan ra’ayi?
A cikin shirin Podcast na Dokin Karfe TV, Hon. Nuhu Abdullahi ya bayyana cewa Shugaba Tinubu yana da matukar ƙauna da goyon bayan ‘yan Najeriya, musamman ma ‘yan Arewa.
Nuhu Abdullahi ya ce Tinubu mutum ne mai cika alƙawari; idan ya ce zai yi abu, ba zai ja baya ba.
Ya ƙara da cewa abubuwan da Shugaban ƙasa Tinubu ya ce zai yi a Arewa, ga su nan yana aiwatarwa a ƙasa ana gani a ido.
Nuhui, ya ƙara sa ‘yan Arewa suna ƙaunashi fiye da kowane shugaban da ya gabata.






