Dambarwar Sarautar Kano: Ana Shirin Tsige Sarki Sunusi Da Nada Nasiru Ado Bayero A Matsayin Sarkin Kano


Ana ta kara zafafa muhawara tsakanin manyan jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki a harkar masarautar Kano game da batun sauya Sarkin Kano. Rahotanni daga manema labarai sun nuna cewa akwai yuwuwar a tsige Sarkin Kano, Alhaji Sunusi Lamido Sanusi, tare da nada tsohon Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero OFR, a matsayin sabon Sarkin Kano.

Wata majiya na cikin gwamnati ta bayyana cewa, akwai tattaunawa a tsakanin manyan gwamnatin jihar da masu fada a ji kan walwalar masarautar, amma har yanzu ba a fitar da wata takamaiman sanarwa daga Gwamnatin Jihar Kano ko daga Fadar Masarautar ba.

Yadda Aka Zo Wajen:

Kamar yadda ake iya tunawa, Gwamna Abba Yusuf ya mayar da Muhammadu Sanusi II a kan kujerar Sarkin Kano ranar 24 ga Mayu, 2024. Wannan ya biyo bayan sanya hannu da ya yi a kan sabuwar Dokar Soke Majalisar Masarautar Kano ta 2024, wacce ta rushe masarautu biyar da aka kafa tun 2019, tare da dawo da tsarin masarauta daya da mayar da Sanusi matsayin Sarkin Kano na 16.

Bayan wannan lamari, Sarki Sunusi ya shiga fadar Kofar Kudu kafin Sarki Aminu Ado Bayero ya iso Kano daga wani tafiya, inda shima ya tare a fadar Nassarawa. A yau, kowanne daga cikinsu na ganin shi ne halastaccen Sarkin Kano, kuma magoya bayansu sun raba gari gida biyu.

Wasu cikin magoya bayan jamโ€™iyyar NNPP da suka fi rinjaye, musamman mabiyan darikar Kwankwasiya, sun rungumi Sunusi II a matsayin Sarkin su. ฦ˜arshen ‘yan jamโ€™iyyar APC sun tsaya tare da Sarki Aminu Ado Bayero, suna kallon shi a matsayin halastaccen Sarkin Kano.

Tarihin Nada Sarki Aminu Ado Bayero:

A ranar 9 ga watan Maris, 2020, tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya nada Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano na 15, bayan tsige Muhammadu Sanusi II, tare da kafa sabbin masarautu guda biyar a fadin jihar.


Allah ya zaunar da Kano da Arewa lafiya, ya ba mu shugabanni nagari.

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *