Dr. Fatima Ahmad Aliyu, uwargidan gwamnan jihar Sokoto, ta kaddamar da shirin raba tallafin abinci da kuɗaɗe ga matan da suka haifi ƴan uku a kananan hukumomi 19 don rage musu nauyin rayuwa.
Dr. Fatima Ahmad Aliyu Uwargidan Gwanman Jihar Sokoto, ta kaddamar da shirin tallafin abinci da kuɗi ga matan da suka haifi ƴan uku a kananan hukumomi 19 na jihar.
Kowace uwa ta samu buhunan shinkafa da gero guda biyar, tare da tallafin kuɗi na naira miliyan daya domin rage nauyin kula da jarirain.
Dr. Fatima Ahmad Aliyu ta ce shirin na nuna kulawa ne ga iyaye masu fuskantar ƙalubalen kashe kuɗi da nauyin rainon yaran ƴan ukku.
Wakilai daga dukkan kananan hukumomin sun halarci bikin, inda aka ba iyayen yaran da aka yi wa rajista kayan tallafin.
A cikin jawabin ta a wajen taron rabo, uwargidan gwamnan ta ce wannan somi-taɓi ne, inda ta ce za ta ci gaba da gudanar da tallafi ire-iren wannan lokaci bayan lokaci.






