Haihuwa wata babbar ni’ima ce da Allah Ya bai wa mata.
Amma tsarin jikin mace, musamman ƙugunta (pelvis), yana taka muhimmiyar rawa wajen yadda haihuwa za ta gudana.
A ilimin likitanci, an bayyana cewa ba duk mata suke da irin ƙugu ɗaya ba.
Bambancin ƙugun mace na iya tasiri sosai wajen sauƙin haihuwa ko kuma bukatar yin tiyatar haihuwa wato CS (Caesarean Section).
Nau’o’in Ƙugun Mata
Masana lafiya sun bayyana cewa akwai manyan nau’o’in ƙugun mata guda huɗu da ake gani a jikin mata:
1. Gynecoid Pelvis
Wannan shi ne ƙugu mafi dacewa da haihuwa ta al’ada.
Yana da faɗi da siffar da ke ba jariri damar wucewa cikin sauƙi yayin haihuwa.
2. Android Pelvis
Wannan ƙugu yana kama da na maza.
Wani lokaci yana iya sa haihuwa ta yi wahala, saboda ba ya da faɗi sosai kamar gynecoid.
3. Anthropoid Pelvis
Wannan ƙugu yana da tsayi fiye da faɗi.
Wasu mata masu irin wannan ƙugu suna iya haihuwa ta al’ada, amma wani lokaci haihuwar na iya ɗaukar lokaci.
4. Platypelloid Pelvis
Wannan ƙugu yana da faɗi daga gefe amma ba shi da zurfi sosai. Saboda wannan dalili, jariri kan iya samun wahalar wucewa ta hanyar haihuwa ta al’ada.
Dalilin Da Yasa Wasu Mata Ke Bukatar CS
Yawancin mata masu ƙugu platypelloid kan fuskanci wahalar haihuwa ta al’ada.
Saboda haka likitoci sukan ba da shawarar a yi Caesarean Section (CS) domin kare lafiyar uwa da jariri.
Haka kuma an nuna cewa irin wannan ƙugu ba kasafai ake samunsa ba.
Kimanin kaso 3 cikin 100 na mata ne kawai suke da irin wannan tsarin ƙugu.
Muhimmancin Duba Lafiya Lokacin Ciki
Domin kauce wa haɗari lokacin haihuwa, yana da muhimmanci mace mai juna biyu ta rika zuwa asibiti domin duba lafiyarta.
Likitoci za su iya gano irin tsarin ƙugunta da kuma hanyar haihuwa mafi dacewa da ita.
Bambancin ƙugun mata abu ne na halitta, kuma yana iya tasiri sosai wajen yadda haihuwa za ta kasance.
Wasu mata suna haihuwa cikin sauƙi, yayin da wasu kuma ke bukatar taimakon tiyata domin kare lafiyarsu da ta jaririnsu.
Abin da ya fi muhimmanci shi ne mace ta rika kula da lafiyarta da bin shawarar likitoci domin samun haihuwa lafiya.
—






