Bidiyon Yadda Furodusa Abubakar Bashir Maishadda Ya Kashe Kudi Sama Da Miliyan Hamsin (₦50,000,000) Wajen Shirya Sabon Fim Dinsa Mai Suna Matan Gida.

Shirin Matan Gida shiri ne da ya ke nuna yadda wasu mata suka zabe mazajen su na sunnah su nema mata a waje a madadin suyi musu kishiya. Acikin shirin yadda jarumar shirin Amaryar Tiktok ke fasa gilashin motan mijinta, bayan sun hadu dashi a hanya ya dauko wata kyakyawar budurwar.

cigaba da karantawa don ganin yadda zata kaya a shirin.

Sabon fim ɗin na forodusa Mai Shadda ya kunshi fitattun jarumai kamar su Ali Nuhu, Yakubu Muhammad, Sani Danja, Sadiq Sani Sadiq, Ali Rabiu Ali, Falalu Dorayi, Bilal Mustapha, Aisha Najamu, Meerah Shuaib, Jamila Rani, Minal Ahmad, Maryam KK, Amal Umar, Farida Abdullahi da sauransu.

Tabbas an zuba kuɗi sosai wajen kayan aiki, wuraren daukar film din, da kayan da aka saka na suturu, da kuma ingantaccen tsarin labari.

A dandalin daukar shirin Mai Shadda yayi kokari wajen daukar nauyin ci da sha na jarumin shi cikin girmamawa don kowa yaci ya koshi a zamanance, inda ya kaisu wani babban wajen cin abinci da shakatawa da ake kira ”Deluna” a cikin Birnin Kaduna.

Shin wannan babban jarin zai kawo sabuwar alaka tsakanin Kannywood da masana’antar fim ta duniya, ko kuwa haɗarin kuɗi ne kawai?

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *