ArewaJazeera
  • About
  • Blog
  • Contact
  • FAQ
  • Home
Monday, March 2, 2026
  • Login
No Result
View All Result
No Result
View All Result
ArewaJazeera
No Result
View All Result
Home Category 2

Dalilan Da Zasu Sa Ka Fara Yin Asuwaki Tun Daga Yau

Malamar Aji by Malamar Aji
February 19, 2026
in Category 2
0
Dalilan Da Zasu Sa Ka Fara Yin Asuwaki Tun Daga Yau

Idan ba ka yin asuwaki, lokaci ya yi da za ka fara daga yau.

Ba kawai don tsabtace hakora ba ne, har ma don kare lafiyar jikinka da samun lada a wajen Allah.

Me yasa ya kamata ka koma yin Asuwaki?

A yau, yawancin burushin zamani da toothpaste suna dauke da wasu sinadarai kamar Triclosan, wanda wasu bincike suka nuna yana iya shafar tsarin sinadaran jiki (hormonal disruption).

Duk da cewa ana amfani da shi wajen kashe kwayoyin cuta, akwai muhawara kan illolinsa ga lafiyar dan Adam.

Shi kuwa Asuwaki, musamman na bishiyar Salvadora persica (wanda aka fi sani da miswak), ba shi da irin wadannan illoli.

A fannin ilimin magungunan tsirrai (Pharmacognosy), an tabbatar da cewa yana dauke da sinadarai masu amfani kamar:

Antibacterial agents – masu kashe kwayoyin cutar da ke janyo rubewar hakora

Fluoride da Silica – masu karfafa hakora da sanya su haske

Essential oils – masu taimakawa wajen magance warin baki da inganta tsaftar baki

Amfanin Asuwaki Ga Lafiyar Jiki

Mutane da dama sun bayar da rahoton cewa yin asuwaki yana taimakawa wajen rage wasu matsalolin ciki, domin sinadaransa na haduwa da yawu su shiga ciki suna aiki.

Haka kuma, ana danganta shi da:

Rage warin baki

Saukaka ciwon kai

Rage kasala

Inganta lafiyar maza

Duk da haka, yana da kyau a tuna cewa asuwaki kari ne ga tsaftar baki, ba maye gurbin shawarar likita ba idan akwai matsalar lafiya mai tsanani.

Asuwaki Sunnah Ce

Baya ga amfanin lafiya, asuwaki babbar sunnah ce ta Manzon Allah (SAW).

Manzon Allah (SAW) ya ce:

> لَوْلاَ أَنْ أَشُقَّ عَلَى أُمَّتِي لأَمَرْتُهُمْ بِالسِّوَاكِ عِنْدَ كُلِّ صَلاَةٍ

Ma’ana: “Da ba don kada in tsananta wa al’ummata ba, da na umarce su da yin asuwaki a lokacin kowace sallah.”

Haka kuma ya ce:

> السِّوَاكُ مَطْهَرَةٌ لِلْفَمِ مَرْضَاةٌ لِلرَّبِّ

Ma’ana: “Asuwaki tsarkakewa ne ga baki, kuma abin neman yardar Ubangiji ne.”


Asuwaki ba kawai don goge hakori aka samar da shi ba.

Sunnah ce mai dauke da lada, tsafta, da kuma amfanin lafiya.

Idan kana son bin koyarwar Manzon Allah (SAW) tare da kula da lafiyarka, ka sanya asuwaki ya zama abokin tafiyarka na yau da kullum.

Wallahu Ta’ala A’alam.

—

Danna Nan Don Samun Wasu Muhimman Abubuwan

Tags: #asuwaki #ramadan #wankebaki #brushdaasuwaki

Related Posts

Yadda Mai Azumi Zai Tara Lada Biyu A Ranar Juma’a (Azumi + Juma’a)
Category 2

Yadda Mai Azumi Zai Tara Lada Biyu A Ranar Juma’a (Azumi + Juma’a)

February 20, 2026
Me Yasa Nake Jin Ƙishirwa Sosai Duk Da Na Sha Ruwa A Sahur?
Category 2

Me Yasa Nake Jin Ƙishirwa Sosai Duk Da Na Sha Ruwa A Sahur?

February 18, 2026
Ina Azumi Na Yi Mafarki Maniyyi Ya Fito Min — Ya Azumina Fa?
Category 2

Ina Azumi Na Yi Mafarki Maniyyi Ya Fito Min — Ya Azumina Fa?

February 18, 2026
Abunda Ya Kamata Kuyi Ana Ganin Watan Ramadan
Category 2

Abunda Ya Kamata Kuyi Ana Ganin Watan Ramadan

February 17, 2026
Miji Na Yana Son In Ringa Tsotsar Gabansa — Shin Ya Halasta A Musulunci?
Category 2

Rashin Ƙarfin Mazakuta: Dalilai, Yadda Ake Gane Matsalar, Da Hanyoyin Magance Rashin Mikewar Gaba

January 21, 2026
Category 2

How Arewa’s Entertainment Industry is Booming

November 10, 2025

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • About
  • Blog
  • Contact
  • FAQ
  • Home

© 2025 ArewaJazeera.com

No Result
View All Result
  • About
  • Blog
  • Contact
  • FAQ
  • Home

© 2025 ArewaJazeera.com

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In