Yin binciken nono da kai, wanda ake kira Breast Self-Examination (BSE), hanya ce mai muhimmanci da kowacce mace ya kamata ta koya.
Wannan dubawa tana taimakawa mace ta san yadda jikinta yake a al’ada domin ta iya gano duk wani canji da wuri kafin matsala ta tsananta.
Ana iya yin wannan dubawa da kanta ko kuma mijinta ya taimaka mata, amma a kiyaye cewa ana nufin miji ne a cikin aure.
Lokacin da ya fi dacewa mace ta yi wannan dubawa shi ne kwanaki biyar zuwa bakwai bayan haila ta ƙare, saboda a wannan lokaci nono baya kumbura sosai.
Idan mace ba ta yin haila, yana da kyau ta zaɓi rana ɗaya a kowane wata ta rika yin dubawar a kai a kai.
Dubawar tana farawa ne da kallo a gaban madubi.
Mace za ta tsaya ta duba nononta a hankali tana lura da ko akwai wani canji a girma ko siffa, ko akwai kumburi, ramuka a fata, ko sauyin launi.
Haka kuma ya kamata ta lura idan nono ya ja ciki ko ya karkace daga yadda yake a al’ada.
Bayan haka sai a duba nonon da hannu.
Ana iya yin wannan a tsaye ko lokacin wanka, domin a lokacin fata tana da laushi.
Ana amfani da yatsun hannu uku wajen matsawa a hankali a zagaye ko daga sama zuwa ƙasa, tare da tabbatar da cewa an duba dukkan nono, ƙarƙashinsa, da kusa da hammata.
Wannan matsawa ana yin sa a hankali, da matsakaicin ƙarfi, sannan da ɗan ƙarfi kaɗan domin jin ƙasan nono.
Haka kuma yana da kyau a sake yin dubawar a kwance a kan gado.
Mace za ta kwanta ta ɗaga hannun gefen nonon da take dubawa, ta sa matashi a ƙarƙashin kafada, sannan ta sake duba nonon kamar yadda ta yi a baya.
Dole ne a duba kan nono ma ta hanyar matsawa a hankali domin ganin ko wani ruwa yana fitowa.
Abubuwan da ya kamata su tayar da hankali sun haɗa da ƙulli da baya ɓacewa, zafi mai ɗorewa, kumburi, fata da ta yi kama da bawon lemu, ko wani ruwa da ke fitowa daga nono musamman mai jini.
Idan mace ta lura da ɗaya daga cikin waɗannan, ya kamata ta je asibiti da gaggawa domin a duba ta.
Yin wannan dubawa ba yana nufin mace ba za ta je asibiti ba ne.
A maimakon haka, yana taimaka mata ne ta san jikinta da kyau.
Dubawar likita da gwaje-gwaje kamar ultrasound ko scan suna da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da lafiyar nono.
Ana ba da shawarar mace ta fara yin binciken nono tun daga shekara ashirin, tana yin sa sau ɗaya a kowane wata.
Wannan yana taimaka mata ta fahimci yadda nononta yake a al’ada domin idan wani canji ya faru ta gano shi da wuri.
Idan akwai tarihin cutar nono a cikin iyali, ya fi kyau a fara kula da wuri tare da zuwa asibiti akai-akai.
Kuma idan mace ta ga wani abu dabam kafin ta kai shekara ashirin, bai kamata ta jira ba — ya dace ta nemi kulawar likita nan da nan.
A takaice, kula da lafiyar nono alhaki ne na kowacce mace.
Sanin jiki da yin dubawa a kai a kai na iya taimakawa wajen gano matsala da wuri da kuma kare lafiya.






