A wasu lokuta budurwa na iya lura cewa wani farin ruwa yana fitowa daga kan nononta.
Wannan abu kan jawo tsoro da damuwa, musamman ga wacce ba ta taɓa yin ciki ko haihuwa ba.
Amma shin wannan al’ada ce?
Kuma me ke haddasa hakan?
A zahiri, ruwan nono yawanci yana fitowa ne lokacin da mace ke da ciki ko bayan ta haihu. Idan budurwa ta ga wani ruwa yana fitowa daga nono, musamman idan sai ta matsa, a mafi yawan lokuta ba cikakken ruwan nono ba ne, amma yana iya zama alamar sauyin hormone a jiki.
Abubuwan Da Ka Iya Haddasa Hakan
Ɗaya daga cikin manyan dalilai shi ne rikicewar hormone, musamman hormone da ake kira prolactin.
Wannan hormone na da alhakin samar da ruwan nono, kuma yana iya ƙaruwa a jikin mace ko da ba ta taɓa aure ko haihuwa ba.
Haka kuma, yawan matsa kan nono ko wasa da nipples na iya tada jijiyoyi da glands ɗin da ke nono, wanda hakan kan sa ruwa ya rika fitowa.
Wasu magunguna ma na iya haifar da wannan yanayi, musamman magungunan damuwa, na barci, ko waɗanda ke shafar hormones.
Akwai kuma yanayin da ake kira benign galactorrhea, wato matsalar gland ɗin nono da ba cancer ba ce, amma tana bukatar a duba ta a asibiti.
A wasu lokuta, matsalar thyroid (musamman hypothyroidism) na iya taka rawa wajen haifar da wannan matsala.
Yaushe Ya Zama Abin Damuwa?
Ya kamata a ɗauki lamarin da muhimmanci idan:
– Ruwan yana fitowa ba tare da an matsa nonon ba
– Yana fitowa daga nono ɗaya kawai
– Yana da launin ja ko ruwan kasa
– Yana tare da ciwo ko kumburi
Wadannan alamomi na iya nuna cewa akwai bukatar a ga likita cikin gaggawa.
Me Ya Kamata A Yi?
Abu na farko shi ne a daina matsa kan nonon.
Sannan a je asibiti domin a yi gwaje-gwaje kamar prolactin test da thyroid test.
Likita ne kawai zai iya tabbatar da ainihin dalilin matsalar tare da bada maganin da ya dace.
A Takaice
Ba al’ada ba ce budurwa ta rika fitar da ruwan nono.
Amma a mafi yawan lokuta, matsalar na da alaƙa da hormone kuma ba lallai ba ce ta zama mai tsanani idan an gano ta da wuri kuma an bi magani yadda ya kamata.






