A ranar, na dawo gida jim kadan bayan tafiyata zuwa wajen aiki.
Dalilin dawowa shi ne na manta wasu muhimman takardu a gida.
Amma abin mamaki ya faru da sauri: da na shiga cikin gidan, na ji muryar matata tana magana da wani mutum wanda ban san shi ba.
Na tsaya a bakin kofa, zuciyata tana bugawa cikin sauri.
‘Ya’yanmu sun tafi makarantar Islamiyya, kuma ni dai na bar gida babu bako.
Don haka ganin mutum a cikin dakina tare da matata ya sa na shiga cikin rudani da fargaba.
A hankali na matsa bakin kofa, sai na lura cewa an kulle ƙofar daga ciki.
Wannan ya kara karfafa fargabar da nake ji:
wanene wannan mutum?
Me yake nufi?
Tambayoyin suna yawo a kwakwalwata.
Duk da fargabar da ke cikin zuciyata, na san matata mutum ce mai aminci, wanda hakan ya sa na kasa yanke hukunci cikin gaggawa.
Na yanke shawarar sanya hannu a mukulli domin buɗe ƙofar.
Amma a daidai lokacin, na ji muryarta cikin nutsuwa tana cewa:
> “Don Allah, ka nutsu. Muyi komai a hankali, babu wata matsala.”
Hannuna ya fara rawa.
Na ja da baya kan kujerar da ke gefena, na zauna a hankali, zuciyata tana bugawa kamar gangar yaƙi.
Na ji muryar mutumin tana magana da matata cikin hankali, yana bayyana tsoronsa, yayin da matata ke kawar da damuwa da kalmomi masu laushi.
Na jingina da bango, zuciyata tana ta tunani da tambayoyi: S
hin wanene tare da matata?
Me suke yi a ɗaki?
Tun yaushe ne wannan ke faruwa?
Hannuna ya miƙa zuwa kofar, a shirye don buɗe ta… Sai kwatsam na ji matata tana kiransa da suna.
A wannan lokacin ne na gane cewa abin da nake shirin gani zai iya canza rayuwarmu gaba ɗaya, amma kuma ina tunanin yadda za a magance rikicin cikin hikima, ba tare da yin gaggawa ko jefa aure cikin barazana ba.
—
Part 5 Na Zuwa Bada Jimawa Ba.






