Fitowar nono a jikin namiji fiye da yadda aka saba (wanda ake kira kumburin nono) na iya ba mutane mamaki ko damuwa.
Wannan matsala ba sihiri ba ce, kuma tana da dalilai na likitanci da suka shafi canjin sinadarai a jiki.
A yawancin lokuta ana iya magance ta idan an gano musabbabinta da wuri.
Daya daga cikin manyan dalilai shi ne canjin hormones a jiki.
Jikin namiji na dauke da sinadarin testosterone, amma idan ya ragu ko kuma sinadarin estrogen (na mata) ya karu fiye da kima, hakan na iya sa nono ya fara kumbura.
Wannan yakan faru a lokacin balaga ko tsufa.
Haka kuma yawan kiba na taka muhimmiyar rawa. Kitsen jiki yana taimakawa wajen samar da estrogen, don haka idan kiba ta yi yawa, zai iya sa nono ya kara girma.
Wannan dalilin ne ya sa wasu maza masu kiba ke fama da irin wannan matsala.
Wani dalili kuma shi ne amfani da wasu magunguna.
Wasu magungunan hawan jini, magungunan damuwa, ko kuma kwayoyin kara kuzari (steroids) na iya haddasa kumburin nono a matsayin illa.
Bugu da kari, shaye-shaye kamar barasa da kwayoyi na iya rikita aikin hormones a jiki.
Shan su na tsawon lokaci yana iya kawo canje-canje da ke sa nono ya fito.
Matsalar hanta ko koda ma na daga cikin dalilai.
Wadannan sassan jiki suna taimakawa wajen daidaita sinadarai.
Idan suna da matsala, hormones na iya rikicewa, wanda zai iya haddasa wannan yanayi.
Hakanan rashin daidaiton thyroid (wani sashen jiki da ke sarrafa metabolism) na iya janyo kumburin nono idan ya yi aiki fiye ko kasa da kima.
A wasu lokuta, gadon hali (genetics) na iya zama sanadi.
Idan akwai tarihin wannan matsala a cikin iyali, akwai yiwuwar wasu su ma su same ta.
A karshe, cututtukan da suka shafi gabobin haihuwa kamar matsalar ƙwayoyin halitta (testicles) na iya rage testosterone, wanda zai haifar da karuwar nono.
Idan namiji ya lura da canji a nononsa, yana da kyau ya garzaya asibiti domin a duba shi.
Wani lokaci matsalar ba mai tsanani ba ce, amma bincike na likita zai taimaka wajen gano ainihin dalili da kuma magani.
Kulawa da lafiya, rage kiba, da kauce wa shaye-shaye na daga cikin matakan kariya da za su taimaka.






