Matan aure da dama suna fuskantar matsalar mazan su saurin zuwan kai yayin jima’i.
Sau da yawa, basu san yadda zasu taimaka musu ba, kuma wasu maza suna jin girman kai wanda ke hana su yarda suna da matsala.
Wannan labarin zai nuna hanyoyi masu sauƙi da mata zasu taimaka wa mazansu domin su iya ɗaukar lokaci a lokacin jima’i.
1. Istimina
Abu na farko da zaki iya yi shine istimina.
Ka cire damuwar jima’i daga ranki.
Yi masa wasa kafin saduwa, sannan bayan ya kawo, ka barshi yayi tsarki ko wanka da ruwan dumi.
Kada ki bashi abu mai sanyi ya sha; ruwan zafi kamar Lipton ko café zai taimaka.
Wannan zai sa gabansa ya sake mikewa ba tare da zuwan kai da wuri ba.
Idan mace zata rika yi masa wannan a kullum har na mako guda, zai iya daina saurin zuwan kai.
—
2. Kada Ki Gajiya
Yawan jima’i na taimaka sosai.
Yin jima’i a kalla sau 3 zuwa 4 a mako na tsawon wata guda zai iya rage saurin zuwan kai.
Ka kasance mai hakuri, kada ki gaji wajen kusantar mijinki da soyayya.
—
3. A Hankali
Kada ki yi gaggawa ko matsa masa sosai a lokacin jima’i.
Yin jima’i a hankali da tsanake zai taimaka wa namiji ya jima ba tare da zuwan kai da wuri ba.
—
4. Ni’ima da Yanayin Gabansa
Mace mai yawan ni’ima a tare da ita tana sa namiji ya kawo a hankali.
Ruwan gaban mace yana taimaka masa wajen jin daɗi.
Kada ki bari gabanki ya daskare kafin mijinki ya sadu dake; tabbatar komai a tsabta.
—
5. Yanayin Saduwa
Wasu yanayin kwanciya na sa maza zuwa da wuri:
Mace ta hau namiji a rigingine ko wasu yanayi masu sauri.
Don haka, guji waɗannan yanayin idan ana son tsawaita lokacin jima’i.
—
Idan ma’aurata zasu baiwa juna lokaci da hakuri, babu shan magunguna, suna iya samun waraka daga wannan matsala.
Mata su fahimci cewa su ne ke da ikon taimakawa, don haka ku bi matakan cikin hakuri domin mazanku su iya bankwana da saurin zuwan kai.
—






