Kamar yadda kamfanin Abnur entertainment karkashin jagorancin Abdul Amart Mai Kwashewa, suka saba duk ranar Lahadi suna kawo muku sabon shirin Manyan Mata.
wannan satin shirin Manyan Mata yazo da sabon salo duba da irin saukin rayuwa da Karima ta fara samu a shirin.
Manyan Mata shiri ne da ke haskaka rayuwar mata da kalubale da suka fuskanta, tun daga zaman iyali, neman aure, har zuwa illolin cin haram ga dangi da iyali.
Wannan sabon Episode yana ɗauke da darasi da yake faɗakar da iyaye da matasa.





