Sexual headache wani irin ciwon kai ne da wasu mutane ke fuskanta yayin jima’i.
Yawanci ciwon kan yana farawa ne yayin da mutum ke ƙara shiga yanayin sha’awa, ko kuma a daidai lokacin inzali.
Wasu mutane suna jin ciwon yana tasowa daga wuya zuwa kai a hankali, yayin da wasu kuma ke jin sa da ƙarfi kwatsam.
Duk da cewa mutum na iya ci gaba da jin daɗin jima’i, ciwon kan kan zama abin damuwa sosai.
Jima’i a zahiri motsa jiki ne. A lokacin, bugun zuciya da hawan jini kan ƙaru, jiki kuma ya ɗumi.
Wannan canjin a jiki na iya jawo matsewa da buɗewar jijiyoyin jini a kai, wanda a wasu mutane ke haddasa ciwon kai.
A wasu lokuta ciwon kan kan tafi bayan mintuna kaɗan da gama jima’i.
Amma ga wasu, yana iya ɗaukar kwanaki 2 zuwa 3 kafin ya lafa.
Wannan na iya sa mutum ya fara tsoron kusantar abokin aurensa duk da yana so.
Wannan matsala ta fi yawan faruwa ga mutanen da ke fama da migraine (ciwon kai na gado), wanda yawanci yana shafar ɓangaren kai guda tare da jin haske ko duhu-duhu a ido.
Haka kuma mata na iya fuskantar wannan matsala fiye da maza.
Muhimmin abu shi ne: sexual headache sananniyar matsala ce a likitance.
Ba alamar asiri ko wata cutar boyayya ba ce. Idan kana fuskantar irin wannan ciwon kai, yana da kyau ka je asibiti ka ga likita.
Bayan cikakken bincike, likita na iya ba da maganin rigakafi da ake sha kafin jima’i wanda zai taimaka rage ko hana tashin ciwon.
Yana da muhimmanci mu guji jingina matsalolin lafiya da camfi.
Neman taimakon likita da wuri na taimakawa rage wahala da kiyaye zaman aure cikin kwanciyar hankali.
Gargaɗi: Wannan bayani an rubuta shi ne domin ilimantarwa kawai.
Ba ya maye gurbin shawarar likita.
Duk wanda ke fama da matsalar ciwon kai mai tsanani ya kamata ya tuntubi ƙwararren likita.






