Mafi yawan ma’aurata masu neman haihuwa sukan firgita idan suka ga maniyyi yana zubowa daga farji bayan saduwa.
Wasu matan ma suna tunanin cewa hakan yana nufin ba za a samu ciki ba.
Amma a hakikanin gaskiya, wannan lamari na dabi’a ne kuma ba matsala ba ce a yawancin lokuta.
Menene ainihin ke faruwa?
Bayan namiji ya fitar da maniyyi a cikin farjin mace, ba duka maniyyin ne ke shiga mahaifa ba.
Abin da jiki baya bukata ne kawai yake komawa waje.
A cikin miliyoyin kwayoyin halittar maniyyi (sperm), kaɗan ne kawai ake bukata su yi tafiya zuwa mahaifa domin haduwa da ƙwai.
Wannan tafiya tana farawa cikin mintuna kaɗan bayan saduwa.
Don haka ko da wani ɓangare ya zubo waje, sperm ɗin da ake bukata sun riga sun fara tafiya.
Shin wannan matsalar mace ce ko miji?
A mafi yawan lokuta:
Ba matsalar mace ba ce, domin farji ba wuri ne da zai riƙe duk wani ruwa gaba ɗaya ba.
Ba matsalar miji ba ce, muddin maniyyinsa yana da lafiya kuma yana da isasshen sperm.
Zubowar maniyyi bayan saduwa al’amari ne na dabi’a ga kusan kowace mace.
Yaushe ne za a damu?
Ana iya buƙatar ganin likita idan:
An shafe lokaci mai tsawo ana saduwa ba tare da samun ciki ba
Akwai zafi ko wata matsala yayin jima’i
Ana zargin matsalar lafiyar haihuwa ga ɗaya daga cikin ma’aurata
Shawarwari ga ma’aurata masu neman haihuwa
Mace ta kwanta a bayanta na mintuna 10–15 bayan saduwa
A guji wankewa nan take bayan jima’i
A kula da lafiyar jiki da abinci mai gina jiki
A rage damuwa, domin damuwa na iya shafar haihuwa
Zubowar maniyyi bayan saduwa ba alamar gazawa ba ce kuma ba yana nufin ba za a samu ciki ba. Yana daga cikin tsarin halittar jiki.
Muhimmanci shi ne lafiyar sperm da kuma lokacin saduwa daidai da lokacin fitar ƙwai.






