A daren yau, Soja Yarima ya tsira daga ƙoƙarin hallaka shi bayan wasu da ba a san ko su waye ba suka biyoshi a motoci biyu kirar Hilux da ba su da lamba, daga gidan mai NIPCO zuwa Gado Nasco Way a Abuja. Sojan ya kware wajen kaucewa har ya samu mafaka.
A daren yau lahadi an sami rikici a birnin Abuja, inda Soja Yerima ya sha da kyar bayan wani ƙoƙari da wasu mutane masu fuska a rufe suka yi na hallaka shi.
Rahotanni sun nuna cewa mutanen suna cikin motoci biyu kirar Hilux masu ba da lamba, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Lamarin ya faru ne a kusa da gidan mai NIPCO dake kan titin Expressway a Abuja, inda Soja Yarima ya lura da motoci biyu da suka biyo shi.
Mutanen da ke cikin motar sun rufe fuskokinsu, suna kokarin binsa har zuwa hanyar Gado Nasco.
A cewar wasu majiyoyi na rundunar soja, Soja AM Yerima ya nuna kwazo da kwarewa wajen kaucewa wadannan motoci, har ya samu mafaka a wuri mai aminci.
Ba a riga an gano ko su waye mutanen da suka kai kokarin wannan hari ba, amma hukumomi sun fara bincike don gano ainihin dalilin da ya sa aka yi wa Soja Yarima kwanton bauna.
Wannan lamari ya tayar da hankalin masu sauraron labarai, inda ake tambaya kan tsaro da dalilan da suka sa aka kai harin soja wanda aka fi sani da mutumin da ya karfafa sojoji a zukatan ‘yan Nijeriya.
A yanzu haka, Soja Yarima yana cikin koshin lafiya a wuri mai aminci, yayin da rundunar tsaro ke ci gaba da bin diddigin lamarin don tabbatar da gaskiya da kare lafiyar jama’a.






