Lauyan kare hakkin bil’adama, Omoyele Sowore, ya bayyana cewa bai dace a cigaba da tsare Sheikh Abduljabbar saboda sabanin fahimta da gwamnati, yana mai kira ga gwamnatin ta sake shi.
Ya zama wajibi a saki Sheikh Abduljabbar, inji Sowore ya sha Alwashin yin fafutuka dan ganin an saki Malamin
Sowore ya bayyana cewa tsare Sheikh Abduljabbar bai kamata ba, domin abinda ke tsakaninsa da gwamnati kawai sabanin fahimta ne.
Ya roƙi gwamnati da ta sake shi tare da jaddada muhimmancin adalci da kare ’yancin dan Adam.






