Jima’i ba wai kawai yana kawo jin dadi ba ne, har ma yana kara kusanci da soyayya tsakanin ma’aurata.
Amma domin soyayya ta dore kuma juna su kara fahimtar junansu, akwai wasu halaye da ma’aurata suka kamata su yi bayan kammala jima’i.
Ga wasu abubuwa 10 da zasu taimaka:
—
1. Yiwa Juna Godiya
Yiwa juna godiya bayan jima’i yana nuna cewa kowanne daga cikin ma’aurata ya bayar da gudummawa.
Wannan na kara dankon soyayya da jin dadi.
2. Tsaftace Al’auran Juna
Bayan jima’i, yana da kyau ma’aurata su tsaftace junansu kafin su shiga wanka.
Wannan na karfafa kulawa da juna, kuma yana nuna ladabi da mutunta juna.
3. Yin Wanka Tare
Shiga wanka tare bayan jima’i yana kara soyayya, jin dadi da kuma cika juna da kulawa.
Hakan na taimakawa wajen kara dankon juna.
4. Ciyar Da Juna
Cin abinci bayan jima’i yana kara jin dadi.
Ko daya daga cikin ma’auratan ba ya jin sha’awar ci, ya kamata su kasance tare suna ciyar da junansu a matsayin alamar soyayya.
5. Tattaunawa Akan Jima’i
Bayan jima’i, yana da kyau ma’aurata su tattauna abubuwan da suka ji, abinda suka so da abinda basu so.
Wannan yana taimakawa wajen fahimtar juna da inganta rayuwar aure.
6. Kwanciya Tare
Kwanciya tare bayan jima’i yana kara shakuwa da kusanci.
Kada ma’aurata su rabu nan take bayan jima’i; lokaci ne na haduwa da soyayya.
7. Rungumar Juna
Rungumar juna bayan kwanciya na karawa ma’aurata jin dadi da soyayya. Wannan yana nuna kulawa da juna a zahiri.
8. Yiwa Juna Kalaman Soyayya
Yiwa juna kalamai masu dadi da shafa juna yana kara jin dadin junansu. Wannan na karfafa soyayya da gamsuwa.
9. Sumbatar Juna
Kada ma’aurata su bar barci ba tare da sumbatar karshe ba. Wannan “good night kiss” yana da tasiri wajen karfafa soyayya da shakuwa.
10. Kulawa Da Juna
Duk lokacin bayan jima’i, ma’aurata su tabbatar suna kula da juna.
Wannan na taimakawa wajen inganta rayuwar aure da dorewar soyayya.
—






